14 Mayu 2022 - 20:16
An Yi Tir Da Isra’ila Kan Farmawa Masu Rakiyar Gawar Shireen

Tun baya hatsaniyyar data faru yayin jana’izar ‘yar jaridar nan ta Al’Jazeera, Shireen Abu Akleh, bangarori da dama ke ci gaba da yin tir da jami’an tsaron Isra’ila kan farmawa masu rakiyar gawar ‘yar jaridar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce sun kadu da abunda ya faru yayin kutsen ‘yan sanda Isra’ila a cikin dandazon masu rakiyar gawar.

Kungiyar tarayyar turai ma ta yi tir da halayen da ‘yan sanda na Isra’ila suka nuna na rashin da’a ga masu rakiyar gawar, da kuma dauka matakai da basu da wani amfani.

Shi ma babban sakataren MDD, ya ce ya kadu matuka da abunda ya gani yayin jana’izar ‘yar jaridar Shireen Abu Akleh da aka bindige yayin samamen sojojin Isra’ila a yankin na Jenin dake yankin gamar yamam da kogin Jordan a ranar 11 ga watan Mayun nan.

Gidauniyar Desmond Tutu, a Afrika ta Kudu, ta fitar da sanarwar allawadai da abunda ya faru wanda ta ce yana tuna abunda ya faru na nuna wariya a Afrika ta Kudun.

Lamarin dai ya faru ne ranar Juma'a a yankin Jenine, yayin jana'izar 'yar jardair ta tashar Al'Jazeera, inda 'yan sandan na Isra'ila suka dinga harbi da dukan masu jana'izar, ciki har da masu dauke da gawarta, lamarin da ya sa gawar ta kusa faduwa kasa.

A nata bangare Isra’ila ta fitar da wata sanar a yau Asabar cewa zata binciki ‘yan sanda ta kan ainahin abunda ya faru yayin jana’izar.

342/